Moyes ba zai yi kwantai ba - Martinez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sallami Moyes daga Man U a ranar Talata

Manajan kulab din Everton Roberto Martinez ya ce David Moyes ba zai jima ba zai sake komawa horadda 'yan kwallo.

Moyes wanda ya jagoranci Everton zuwa mataki na hudu a gasar Premier League a shekaru 11 a kulab din, ya hade da Man U a kakar wasannin data gabata amma an sallame shi a ranar Talata.

'Ina da tabbacin cewa a shirye yake ya sake kama wani aikin, kuma na tabbata ba zai ki wani tayin ba', in ji Martinez.

Ya kara da cewa za a rika tunawa da shi kuma 'zamu cigaba da yi masa godiya ga aikin da ya yi mana a kulab dinmu'.

Moyes shine ya lashe lambar yabo ta kungiyar masu horar da 'yan wasan kulob kulob na League har sau uku a Everton, inda kuma ya lashe wasanni 218 daga cikin 518.