Renard ya nisanta kansa daga Morocco

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Renerd na tare da Sochaux a Faransa a yanzu

Mai horar da 'yan wasan Sochaux Herve Renard ya nisanta kansa daga rahotannin dake cewa zai iya zama kochin Morocco na gaba.

Morocco na bukatar nada wanda zai maye gurbin Rashid Taoussi na dindindin, bayan da aka sallame shi a bara.

An dai yi imanin cewa Atlas Lions na zawarcin Renard dan shekaru 45 wanda ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2012 tare da Zambia.

Sai dai Renard ya shaidawa BBC cewa 'a yanzu dai ina Faransa kuma abinda nake baiwa fifiko farko shine zama a Turai ko kuma komawa zuwa wani kulab din mai kyau'.