Lacina Traore na Ivory Coast ya warware

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan labari ne mai dadin ji ga 'yan kasar Ivory Coast

Manajan kulob din Everton Roberto Martinez ya yiwa 'yan kasar Ivory Coast albishir inda ya ce dan wasan gaban sa lacina Traore wanda yai fama da rauni a yanzu yana warkewa.

Martinez ya ce dan wasan zai iya shiga cikin tawagar 'yan wasan da zasu taka gasar cin kofin kwallon kafar duniya a Brazil.

Amma sai dai Martinez ya kara da cewa Traore a yanzu ba zai iya sake bugawa Everton wasa ba.