'Ina alfahari da jan ragamar United'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ryan Giggs ya dade a Old Trafford

Kocin riko na Manchester United, Ryan Giggs ya ce jagorancin kungiyar shi ne "lokaci mafi alfahari gare ni a rayuwa ta".

Dan shekarun 40, zai jagoranci United a wasanni hudun da suka rage a kakar wasa ta bana.

Giggs wanda shi ne dan kwallon da ya fi kowanne samun nasarori a United, ya ce yanason ya tsallakar da kungiyar zuwa gasar Europa a kakar wasa mai zuwa.

"Ina alfahari, ina jin dadi amma kuma ina dan jin tsoro," in ji Giggs.

United za ta dauki bakunci Norwich a gasar Premier a ranar Asabar.

Karin bayani