Tsohon kocin Barca Vilanova ya rasu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Margayi Tito Vilanova

Tsohon Kocin Barcelona Tito Vilanova ya rasu yana da shekaru 45 sakamakon doguwar jinya kan cutar daji.

Vilanova na fama da cutar daji ko cancer a makogwaronsa abinda ya sa aka yi masa tiyata a watan Nuwambar 2011, amma sai cutar ta kara taso masa a watan Disambar 2012.

Ya ajiye mukaminsa na kocin Barca a watan Yuli don ci gaba da magani, inda Gerardo Martino ya maye gurbinsa.

Sanarwar da Barcelona ta fitar ta ce " FC Barcelona na juyayin rasuwar Tito Vilanova mai shekaru 45".

Karin bayani