Man' United ta musanta daukar sabon Koci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya dai an ce Van Gaal na shirin koma wa Tottenham ne a zaman koci.

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United ta musanta rahoton wata jaridar kasar Holland cewa Louis Van Gaal ya amince ya zamo sabon kocinta.

Masu kuriar caca dai sun zabi kocin dan kasar Holland mai shekaru 62 da haihuwa a zaman wanda suke hasashen ya maye gurbin David Moyes wanda aka sallama ranar Talata.

Wata Jaridar kasar Holland De Telegraaf ta ba rahoton cewa ya sa hannun kan wata kwataragi da United din, amma kungiyar ta musanta labarin.

''Mu ba mu dauki wani sabon koci ba. Duk sa'adda mu ke da wani batu da muke son kafafen watsa labarai su fada, za mu sanar'' Inji mai magana da yawun kungiyar.

A halin yanzu dai Van Gaal na da kwantaragi da kungiyar kwallon kafa ta kasar Holland har zuwa karshen gasar cin kofin duniya a kasar Brazil.

Karin bayani