Arsenal ta buge Newcastle 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne karo na shida da Newcastle ke rashin nasara

Arsenal ta ci gaba da zama daram a matsayi na hudu a Premier da zai kai ta gasar Zakarun Turai bayan ta doke Newcastle 3-0.

Laurent Koscielny ne ya fara jefa kwallo a ragar bakin a minti na 26, kafin kuma a minti na 42 Mesut Ozil ya kara ta biyu.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma a minti na 66 Ozil ya dauko wata kwallo ta gefe Olivier Giroud ya jefa ta raga da ka.

Arsenal ta ci gaba da kasancewa ta hudu da maki 73 a wasanni 36, yayin da Newcastle take matsayi na tara da maki 46.

Karin bayani