Ferdinand na son zama a Man United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ferdinand ya ce dukkanin su suna da alhakin halin da Manchester United ke ciki a bana

Rio Ferdinand na son cigaba da zama a Manchester United a kaka ta gaba ko da wanene ya kasance kociyan kungiyar.

Dan wasan mai shekara 35 zai kammala kwantirginsa da United a karshen kakar nan kuma ana ganin zai bar kungiyar.

To amma kuma yanzu ya ce, ''zan cigaba da wasa ko a nan ne ban sani ba, amma ina fatan a nan ne.''

Korarren kocin kungiyar Moyes ya sa shi a farkon wasan Premier sau tara amma kocin rikon kwarya Giggs ya fara sa shi a cikin wata daya a wasan da suka lallasa Norwich 4-0.

Dan wasan ya nuna rashin jin dadin yadda Moyes ba ya sa shi a wasa sosai, amma ya ce daman haka wasan ya gada.

Ferdinand wanda ya koma Man United daga Leeds shekaru 12 da suka wuce, a kwankinnan ya ce matsayinsu na Premier a bana na ba shi kunya.