Kevin Phililips zai yi ritaya

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Kevin Phillips ya taimaka wa Leicester City da Crystal Palace shiga Premier

Tsohon dan wasan gaba Kevin Phillips zai bar wasan kwallon kafa bayan ya taimaka wa Leicester City ta shiga gasar Premier.

Phillips wanda ya ci kwallon da ta bai wa Crystal Palace damar shiga gasar Premier a bara, a watan Janairu ya koma Leicester.

Dan wasan mai shekaru 40, da ya buga wa Ingila wasanni takwas, zai ci gaba da kasancewa da kungiyar tare da masu horad da 'yan wasa a kaka ta gaba.

Shi ne dan wasan Ingila na karshe da ya ci kyautar Takalmin Zinare na Premier, da ya ci wa Sunderland kwallaye 30 a 1999 zuwa 2000.