Kofin Afrika: Uganda ta koka

Image caption Uganda za ta yi wasanni goma kafin ta samu cancantar zuwa gasar a Moroko.

Kocin Uganda Milutin 'Micho' Sredojevic ya nuna damuwarsa kan rashin tazara mai yawa a wasannin neman zuwa gasar cin Kofin Afrika na 2015.

Kociyan ya ce, ''idan da a Turai ne hakan zai kasance da sauki to saboda wadattun kayayyaki amma a Afrika akwai matsala.''

Kasashe 49 ne za a rage zuwa 15 da za su je gasar a cikin watanni shida kacal.

Uganda za ta hadu da Madagascar a zagayen farko kuma idan ta yi nasara za ta fafata da wadda ta yi galaba tsakanin Mauritania da Equatorial Guinea a zagaye na biyu.

Idan ta yi nasarar tsallake wadannan matakai biyu daga nan za ta shiga rukuni na biyar (Group E) da ya hada da Ghana da Guinea da kuma Togo.