Real Madrid ta yi waje da Bayern 5-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ronaldo ya ci kwallaye 16 ke nan a wasanni goma da ya yi a gasar, da hakan ya sa ya zarta Lionel Messi mai 14.

Real Madrid ta yi waje da Zakarun Turai kuma na Jamus Bayern Munich da ci 4-0, jumulla gida da waje 5-0 a gasar Zakarun Turai.

Wasan da ake yi a birnin Munich shi ne karo na biyu na matakin kusa da karshe na gasar.

Sergio Ramos ne ya fara jefa kwallo a ragar Bayern a minti 16 da shiga fili kafin kuma ya kara ta biyu bayan wasu mintina hudu.

Cristiano Ronaldo ne kuma ya biyo baya da kwallo ta uku bayan wasu mintina 14.

Can ana shirin tashi daga wasan a minti na casa'in sai Ronaldon ya kara sheka kwallo ta hudu a bugun tazara.

A ranar Laraba ne za a yi wasa na biyu na kusa da na karshen karo na biyu tsakanin Chelsea da Atletico Madrid a Stanford Bridge.

Karin bayani