Cech da Terry sun dawo atisaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cech ya ji rauni ne a kafadarsa a wasansu na farko da Atletico Madrid

Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech da dan wasanta na baya John Terry sun dawo atisaye ranar Talata.

'Yan wasan biyu sun ji rauni ne a wasansu na farko na Kofin Zakarun Turai da Atletico Madrid a makon da ya gabata da su ka tashi 0-0.

Suna shirin sake dawowa ne a karawa ta biyu ta wasan na kusa da karshe na gasar ranar Laraba a Stanford Bridge.

Eden Hazard da Samuel Eto'o su ma sun samu damar yin atisayen.

'Yan wasan tsakiya John Mikel Obi da Frank Lampard ba za su buga wasan ba saboda an ba su katin gargadi bibbiyu.

Shi ma kyaftin din Atletico Gabi ba zai yi wasan ba saboda katin gargadin da ya samu, kuma ana sa ran tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Tiago Mendes zai maye gurbinsa.