Pardew na sa ran zama a Newcastle

Hakkin mallakar hoto
Image caption A shekara ta 2012 kungiyar ta bai wa Pardew kwantiragin shekara takwas.

Kociyan Newcastle Alan Pardew ya yi imanin ci gaba da zama a kungiyar duk da rashin nasara sau shida a jere da damuwar magoya baya.

Magoya bayan kungiyar sun nuna damuwarsu matuka a lokacin wasan da Arsenal ta lallasa su 3-0 ranar Litinin.

Pardew ya ce, ''na san cewa ba su ji dadi ba suna cikin bacin rai ba mu yi nasara ba.

Amma kuma ina kallon aikin a matsayin wata dama ta tsawon lokaci gareni. Haka ya kamata ka mayar da hankalinka.''

Pardew wanda ya kammala hukuncin dakatar da shi, shiga fili na wasanni bakwai yana ganin za su kammala gasar da kyakkywn matsayi.