'Akwai matsala a shirin Olympics na Rio'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana fuskantar tsaiko a gine-ginen na Rio

Wani babban jami'i a kwamitin shirya wasannin olympic na duniya IOC ya ce, bai taba ganin shiri mara kyau ba na wasanni kamar na Rio de Janeiro.

A shekara ta 2016 ne birnin Rio na Brazil zai dauki bakuncin wasannin Olympics din.

A wani taron manema labarai da kwamitin ya shirya a Australia, mataimakin shugabansa John Coates, ya bayyana cewa, ana fuskantar koma baya sosai wajen gine-gine, akasin yadda aka tsara tun farko - wasu wuraren ba a ma fara gininsu ba.

Mista Coates yayi gargadin cewa, ba wani shiri na ko-ta-kwana da suka yi, na neman wanda zai karbi bakuncin wasannin idan Brazil ta kasa.

An sami cikas ne saboda irin jinkirin da ake fuskanta, da karuwar farashin kayayaki, da kuma rashin tuntubar juna kamar yadda ya kamata, tsakanin hukumomin Brazil da masu shirya gasar.

Karin bayani