Ana hassada da Chelsea - Schurrle

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andre Schurrle

Dan kwallon Chelsea, Andre Schurrle ya ce masu sukar kungiyarsa saboda salon kwallonsu da Liverpool, suna musu hassada ne kawai.

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya zargi Jose Mourinho da ajiye "motocin bus biyu" a kusa da raga.

Schurrle ya ce " Samun nasara shi ne abin da muka sa a gaba".

A cewarsa wadanda ke zargin Chelsea ba ta iya kwallo ba, suna hassada ne kawai.

Chelsea ta yi irin salon kwallon a wasan da ta tashi babu ci da Atletico Madrid a tsakiyar mako.

Karin bayani