Townsend ba zai buga Gasar Kofin Duniya ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara gasar ta cin kofin duniya ne ranar 12 ga wata Yuni.

Dan wasan kwallon kafa na kasar Ingila Andros Townsend ba zai samu buga Gasar Cin Kofin Duniya ba bayan an bashi hutun makonni 10 saboda raunin da ya samu a kafa.

Za a yi wa Townsend aikin tiyata a kafarsa ta hagu ranar Alhamis sakamakon raunin da ya samu yayin wasan da kungiyarsa ta Tottenham Hotspur ta buga da Stoke City ranar Assabar.

A ranar 12 ga watan Mayu ne Kocin Ingila Roy Hodgson zai sanar da tawagar da za ta wakilci kasar a gasar da za a yi a Brazil.

Ingila za ta fara karawa da kasar Italiya ne a gasar ranar 14 ga watan Yuni; sai da kafin lokacin za ta buga wasanni sada zumunci uku da kasashen Peru da Honduras da kuma Equador.

Karin bayani