Atletico ta fitar da Chelsea da 3-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arda Turan dan Turkiyya shi ya kammala cin da kwallo ta uku a minti na 72.

Fatan Chelsea na zuwa wasan karshe na uku cikin shekaru bakwai na gasar kofin Zakarun Turai ya kare bayan da Atletico ta casa ta 3-1.

Yanzu Atletico za ta hadu da abokan hamayyarta Real Madrid a wasan karshe ranar 27 ga watan Mayu a Lisbon, Portugal.

Torres ne ya fara jefa kwallo a ragar tsohuwar kungiyar tasa a minti na 36 da wasa.

Saura minti daya a tafi hutun rabin lokaci sai Adrian Lopez ya rama wa bakin.

Ana minti na 60 ne kuma sai Diego Costa ya kara jefa kwallo ragar Chelsea a bugun fanareti.

Arda Turan dan kasar Turkiyya shi ya kammala cin da kwallo ta uku a minti na 72.

Wannan shi ne karon farko da kungiyoyi biyu daga birni daya za su yi wasan karshe na gasar.

Karin bayani