Courtois ne ya ceci Atletico - Mourinho

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana saran Courtois zai koma Chelsea a kakar wasa ta bana

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce golan da suka baiwa Atletico Madrid aro, Thibaut Courtious shi ne ya hana su zura kwallo a gasar zakarun Turai.

Atletico Madrid ta fitar da Chelsea a zagayen kusada karshe na gasar bayan ta samu galaba da ci 3 da 1 a filin Stamford Bridge.

Mourinho ya ce "Courtious ya ceci Atletico saboda kare kallon da John Terry ya nemi sakawa a raga".

Courtois dan kasar Belgium mai shekaru 21 ya bugawa Atletico Madrid wasanni 150 tun lokacin da Chelsea ta bada aron sa.

A yanzu dai Atletico Madrid za ta hanu ne da Real Madrid a wasan karshe za su hadu a birnin Liston na Portugal a ranar 24 ga watan Mayu.

Karin bayani