Watakila Walker ba zai je Brazil ba

Watakila dan kwallon Ingila, Kyle Walker ba zai buga gasar cin kofin duniya a Brazil ba saboda rauni a kugunsa.

Dan wasan Spurs din ya buga wa Ingila kwallo a wasanni 10 kuma ana saran ya yi hammaya da Glen Johnson a kokarin takawa kasar leda.

Walker mai shekaru 23, bai kara buga kwallo ba tun bayan da ya samu rauni a wasansu da Benfica a ranar 13 ga watan Maris.

Kocin Ingila, Roy Hodgson ya ce "Mun damu matuka saboda sun ce zai yi jinyar makonni shida zuwa goma".

Idan har Walker ba zai je Brazil ba, to watakila Hodgson ya gayyaci Jon Flanagan na Liverpool don maye gurbinsa.

'Yan wasan Ingila da ba za su Brazil ba sun hada da Andros Townsend, Theo Walcott da kuma Jay Rodriguez.

Karin bayani