Ba zan sauya salon wasana ba- Guardiola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pep Guardiola

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya ce ba zai canza salon wasansa, duk cewar ya sha suka saboda Real Madrid ta doke su.

Real ta doke Bayern Munich a filin Allianz Arena da ci 4 da 0 a wasan zagayen kusada karshe na gasar zakarun Turai.

Guardiola ya ce "Na san abinda nake yi kuma na san yadda ya kamata 'yan wasana su taka leda".

Tsohon kocin Barcelona din ne ya lashe kofuna 14 a kakar wasanni hudu a Spain daga shekara ta 2008 zuwa 2012.

Guardiola ya jagoranci Bayern ta lashe gasar Bundeslisga kuma zai buga wasan karshe da Borussia Dortmund a gasar cin kofin kalubale na Jamus.

Karin bayani