CAF ta haramtawa Gambia shiga kowace gasa

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaban CAF Issa Hayatou ta jaddada cewa ba su lamunin irin wannan yaudarar ko kadan.

Kwamitin Zartarwa na Tarayyar kungiyoyin kwallon kafar nahiyar Afrika CAF, ya dakatar da kasar Gambia daga shiga kowace irin gasa na tsawon shekaru biyu, saboda yin karya kan shekarun wasu 'yan wasa.

A watan jiya ne aka fara dakatar da Gambia daga gasar cin kofin nahiyar ta 'yan kasa ga shekaru 20 saboda sa 'yan wasan da shekaru suka wuce 20 su buga mata wasa.

A yanzu kuma a haramtawa Gambiar shiga duk wata gasa da CAF din ke shiryawa cikin har da gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a yi badi.

Hukumar CAF da ta kaddamar da bincike ne kan daya daga cikin 'yan wasanta ne mai suna Ali Sowe wanda aka haifa a watan Yuni 1994, amma sai aka gano an yi masa rijista da hukumar ta CAF bisa cewa an haifeshi ne a shekara ta 1988.

Karin bayani