Lahadi: Wasannin Premier da na La Liga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Terry ya murmure daga raunin da ya ji, kuma zai yi wasan Chelsea da Norwich

A wasan Premier mako na na 36 na Lahadinnan Chelsea ta yi canjaras 0-0 da Norwich, Arsenal kuwa ta doke West Brom da ci 1-0; yayin da a La Liga kuwa Levante ta doke Atletico Madrid 2-0, Almeria kuma ta doke Real Betis 3-2.

Sakamakon wasan Chelsea da Norwich dai ya dakushe duk wata fata da Chelsea ke da ta daukar kambun gasar ta Premier.

Yanzu Arsenal ta tabbata a matsayi na hudu da zai ba ta damar zuwa gasar Zakarun Turai karo na 17 a jere.

Hakan ya kasance ne saboda Everton ta biyar wadda ke hamayya da ita a matsayin, ta yi rashin nasara a wasanta da Man City.