Giggs ya nuna alamun barin Man' United

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Giggs ya kau da yiwuwar buga wa wata kungiya wasa a gaba, sai dai zama koci.

Dan wasan kungiyar Manchester United Ryan Giggs na shirin buga wa kungiyar wasa na karshe bayan da ya nuna alamun cewa zai bar kulob din domin cika burinsa na zama koci.

Giggs mai shekaru 40, ya fara bugawa United wasa ne tun yana dan shekaru 17 a shekarar 1991 inda ya taimaka mata ta ci kofuna 34.

Dan wasan wanda yanzu shi ne kocin kungiyar na rikon kwarya ya ce mai yiwuwa ne wasan da za su buga da Hull City a filin Old Trafford ranar Talata ya zama na karshe da zai buga a kulob din.

Giggs wanda ya buga wa United wasanni 962, ya zamo kocin rikon kwarya ne bayan sallamar David Moyes a watan jiya.

Karin bayani