Juventus ta lashe kambun Serie A

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roma dai na bukatar ta ci wannan wasan ne kafin ta ci gaba da zama cikin masu sa ran lashe kambun.

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta lashe kambun gasar Serie A ta Italiya karon na uku a jere.

Juventus ta samu wannan nasarar ne bayan da Catania ta doke babbar abokiyar hamayyar Juventus din- wadda kuma ke biye mata a teburin gasar wato AS Roma da ci 4-1 ranar Lahadi.

Wannan kashin da Roma ta sha dai ya sa Juventus ta sha gabanta da maki takwas, kuma wasanni bibbiyu ne suka rage ma kowacensu.

A yanzu yaran na Antonio Conte za su yi bukin lashe kambun ne yayin wasan da za su buga ta Atalanta ranar Litinin.

Karin bayani