Suarez ne gwarzon FWA na bana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Suarez zai karbi lambar yabon ne ranar 15 ga watan Mayu a wajen wani buki a birnin London.

Kungiyar marubuta labaran wasannin kwallon ta Ingila ta zabi dan wasan gaba na Liverpool Luis Suarez a zaman gwarzonta na shekara.

Suarez dan kasar Uruguay mai shekaru 27 ya ci kwallaye talatin a gasar Premier wa kungiyarsa da ke fafutukar ganin ta lashe kambun gasar karon farko tun 1990.

Suarez ya dauki kashi 52% na kuri'un da aka jefa yayin da takwaransa na kungiyar Liverpool Steven Gerrard yazo na biyu; sai kuma Yaya Toure na Manchester City ya zo na uku.

Sama ga 'yan jarida 300 ne suka jefa kuri'a don zabar daya daga cikin 'yan takara goma da aka ba da sunayensu domin basu lambar yabon wadda dan wasan Blackpool Stanley Matthews ya fara lashewa a shekara ta 1948.

Karin bayani