Fulham ta nemi afuwan masoyanta

Image caption Magath ya ce tabbas ne za a yi manyan sauye-sauye a kungiyar a cikin watanni masu zuwa.

Manajan Fulham Felix Magath ya nemi afuwa kan doke kungiyar da Stoke City ta yi da ci 4-1, lamarin da ya fitar da Fulham din daga rukunin gasar Premier.

A cikin wata budaddiyar wasika da ya rubuta wa magoya bayan kungiyar, Felix Magath ya lashi takobin ci gaba da rike Fulham din tare da sake gina ta zuwa wata kungiya mai karfin kai wa sama..

"Mu a matsayinmu na kungiya, ni kaina da shugabannin kulob, muna neman afuwa kan gaza tabuka abin kirki" ; inji Kocin dan kasar jamus.

A cewarsa "Gaskiya dai ita ce an fitar da mu daga rukunin Premier, sai dai kuduri da muradina na gina Fulham suna nan daram".

Tsohon kocin na Bayern Munich mai shekaru 60, ya je Fulham ne a watan Fabrairu, inda ya ci wasanni uku kadai a karawa 11 da ya buga a gasar ta Premier.

Karin bayani