Tottenham ta nemi afuwa ga Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham dai ta ce zata bincika ko an yi matsa kutse ne a shafin nata.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Tottenham ta roki afuwa kan saka wani bidiyo a shafinta na Twitter da ke zolayar Liverpool kan yadda ta sha kasa a gasar Premier.

Haka ma kungiyar da ke birnin London ta ce za ta binciki yadda aka yi aka saka bidiyon a shafin nata.

Liverpool ta yi canjaras 3-3 da Crystal Palace ranar Litinin da dare abin da ke zaman kamar ta mika kambun ga Manchester City ne.

An saka wani sako ne da ke cewa ''Aikin rashin tausayi amma mai ban dariya'' tare hoton bidiyon inda Luis Suarez ke kuka a shafin Twitter na tottenham din; amma nan da nan suka cire shi.

Karin bayani