Yadda rikicin Ukraine ya shafi wasanni

Hakkin mallakar hoto unian
Image caption Hukumar Kwallon Kafar za ta kira wani taro domin nazarin inda ya fi dacewa a buga wasan karshen

An sauya wuraren buga wasannin gasar Premier da ta kofin kalubale na kasar Ukraine daga biranen gabashin kasar da kuma tsibirin Crimea saboda rikicin siyasar da ake yi a yankunan.

Dynamo za ta kara da Illichevets a birnin Kiev a maimakon garin Mariupol inda Illichevist ke da mazauni.

Haka ma birnin na Kiev zai karbi bakuncin wasan da za a buga tsakanin Sevastopol da Metalist Kharkiv.

Hukumomin birnin Sevastopol da ke yankin Crimea da Rasha ta mamaye a watan Maris, sun hana buga wasan a garin saboda halin rudanin siyasa da ake ciki.

Birnin Kharkiv a hukumance ya bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Ukraine ta dauke wasan karshe na gasar kofin kalubalen daga birnin saboda hadarin barkewar rikici.

Karin bayani