UEFA za ta ci tarar Man City da PSG

Hakkin mallakar hoto UEFA
Image caption Hukuncin Uefa zai shafi kungiyoyin a gasar zakarun Turai

Bisa dukkan alamu Manchester City da Paris St-Germain za su biya tarar kusan fan miliyan 50 saboda saba ka'idar Uefa kan batun kashe kudade.

BBC ta fahimci cewar watakila a rage adadin 'yan kwallon da kungiyoyin biyu za su fitar don fafatawa da gasar zakarun Turai.

Bayanai sun nuna cewar kungiyoyi kusan tara ne suka saba ka'idar Uefa ka batun cefanan 'yan kwallo.

Idan har hukuncin ya tabbata, adadin tawagar 'yan kwallo da kungiyoyi za su saka a gasar cin kofin zakarun Turai ba zai wuce 21 ba a maimakon 25 da aka saba.

Karin bayani