Brazil: Wa ke tawagar Super Eagles?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kira Odemwingie ne bayan kawo karshe fadan suke da Kocin kungiyar Stephen Keshi.

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa 30 da za su wakilci kasar a Gasar cin Kofin Duniya ta 2014 a Brazil.

Daga cikin 'yan wasan da ke buga wasa a kasashen waje da aka kira dai akwai dan wasan gaba na Stoke City Peter Odemwinge, da na Newcastle Shola Ameobi da kuma Kyaftin din kungiyar Joseph Yobo.

John Mikel Obi na Chelsea da Victor Moses na Liverpool ne ke sama a jerin sunayen 'yan wasa 19 da aka cirato daga cikin wadanda suka buga wa kasar Gasar cin kofin Nahiyar Afrika a bara.

Najeriya dai za ta kara da kasashen Argentina da Iran da Kuma Bosnia a rukuni F a gasar ta cin Kofin Duniya.

Cikakken Jerin Sunayen

Masu tsaron gida:

Vincent Enyeama na Lille FC ta Faransa da Austin Ejide na Hapoel Be'er Sheva ta Isra'ila da Daniel Akpeyi na Heartland da kuma Chigozie Agbim na Gombe United.

'Yan wasan baya:

Elderson Echijile na AS Monaco ta Faransa da Efe Ambrose na Celtin ta Scotland da Godfrey Oboabona na Rizespor ta Turkiya da Azubuike Eguekwe na Warri Wolves da Kenneth Omeruo na Middlebrough ta Ingila da Juwon Oshaniwa na Ashdod FC ta Isra'ila Joseph Yobo na Norwich City ta Ingila Kunle Odunlami na Sunshine Stars

'Yan wasan tsakiya

John Mikel Obi na Chelsea ta Ingila Ramon Azeez na Almeria FC ta Spain Ogenyi Onazai na SS Lazio ta Italiya Joel Obi na Parma ta Italiya Nnamdi Oduamadi na Varese ta Italiya Ejike Uzoenyi na Enugu Rangers Nosa Igiebor na Real Betis ta Spain Sunday Mba na CA Bastia ta Faransa Reuben Gabriel na Waasland-Beveren ta Belgium Michael Babatunde na Volyn Lutsk ta Ukraine

'Yan wasan gaba

Ahmed Musa na CSKA Moscow ta Russia Shola Ameobi da Newcastle United ta Ingila Emmanuel Emenike na Fenerbahce ta Turkiyya Obinna Nsofor na Chievo Verona ta Italy. Peter Odemwingie ta Stoke City ta Ingila Michael Uchebo na Cercle Brugge ta Belgium Victor Moses na Liverpool ta Ingila Uche Nwofor na Heerenveen ta Holland

Karin bayani