Jinkirin nada sabon kocin Man United

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Louis Van Gaal

Manchester United ba za ta sanar da sunnan sabon manajan 'yan wasanta ba a wannan makon.

Bayanai sun nuna cewar kocin Netherlands, Louis van Gaal ne zai zama sabon kocin United, amma kuma shi kocin ya ki amsa tambayoyin manema labarai game da batun.

Da farko an zaci United za ta bayyana wanda zai maye gurbin David Moyes bayan wasanta da Hull a ranar Talata.

Amma kuma BBC ta fahimci cewar watakila sai bayan wasan United a ranar Lahadi tsakaninta da Southampton kafin a bayyana sunnan sabon kocin.

Van Gaal zai sauka daga mukaminsa a Netherlands bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Brazil.

Ana saran kocin United na riko, Ryan Giggs zai tattuna da mahukunta Manchester United a ranar Juma'a domin sannin makomarsa.

Karin bayani