'Ghana na bukatar John Mensah ya dawo'

Image caption 'Yan Ghana na bukatar kyayawan shiri a baya

Tsohon dan wasan Black Stars na Ghana Samuel Osei Kuffor ya ce Ghana na bukatar tsohon Kyaptin John Mensah ya dawo domin samun jagoranci a baya.

Ya ce kowacce tawagar 'yan wasa na bukatar shugaba musamman a bayan ta kuma idan kana da John Mensah akwai tsaro in ji Kuffor.

A ranar Litinin mai horar da 'yan wasan Ghana Kwesi Appiah zai saki sunayen tawagar 'yan wasan da zasu wakilci kasar a Brazil.

Ghana za ta yi wasa a rukuni na G tare da Kasashen Jamus da Portugal da Amurka kuma abinda yafi damun magoya bayan 'yan wasan Black Stars shine 'yan wasan bayan su.