Brazil: Klose na cikin tawagar Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Klose na cikin wadanda zasu je Brazil

Dan wasan gaban Jamus Miroslav Klose ka iya kasancewa dan wasan da zai fi kowa zura kwallaye a gasar cin kofin duniya a tarihi bayan da aka zabe shi cikin 'yan tawaggar da zasu je gasar.

Klose dan shekaru 35 a duniya na bukatar ya zura karin kwallaye biyu domin ya doke tarihin da tsohon dan wasan Brazil Ronaldo ya kafa.

Klose ya ci kwallaye har sau biyar a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 2002 da kuma 2006

Ya kuma zura kwallaye hudu a shekarar 2010 a Kasar Afirka ta Kudu a wasan kusa dana karshe da aka doke su.