Ina son zama Kochin ManU- Van Gaal

Van Gaal Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana yiwa van Gaal kallon shine sabon kochin ManU

Manajan kulab din Netherlands Louis van Gaal ya fadawa BBC cewa yana son zama sabon manajan Manchester United

Ana yiwa Kochin Netherlands mai shekaru 62 kallon shine zai dare kujerar manajan kulab din tun lokacin da aka kori David Moyes a ranar 22 ga watan Afrilu.

Ana dai tsammanin kulab din Manchester United zai tabbatar da nadin sabon Kochin a makon gobe.

Sai dai Van Gaal ya shaidawa manema labarai cewa a jira a ga abinda ManU zasu yanke tukuna.