Blatter zai kara yin takara a 2015

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya- Fifa Sepp Blatter ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar a karo na biyar domin shugabantar hukumar a shekarar 2015.

Dan kasar Switzerland mai shekaru 77 wanda ya ke rike da mukamin tun a shekarar 1998, ya kuma bayyana cewa ba zai sake yin takara ba lokacin da ya koma kan mukaminsa a shekarar 2011 ba tare da hamayya ba.

Blatter ya fadawa jaridar Blick cewa, "Zan sake yin takara. Wa'adi na ya kare amma ban kammala cimma buri na ba."

Za a gudanar da zaben shugaban Fifa ne a birnin Zurich cikin watan Yunin 2015.

A hirarsa da BBC a watan Oktoban bara, Blatter ya musanta batun sake tsayawarsa takara, sai dai ya nuna alamun niyyarsa ta ci gaba da rike mukamin.

Mataimakin shugaban hukumar ta Fifa, Jeffrey Webb da tsohon babban mataimakin sakatare Jerome Champagne sune ake sa ran za su maye gurbin Blutter, amma su duka sun nuna goyon bayan su ga shugaba mai ci din.

Karin bayani