Bakin Mourinho ya ja masa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho

An ci tarar Manajan Chelsea, Jose Mourinho fam dubu goma saboda kalaman da ya yi bayan karawar kungiyarsa da Sunderland a ranar 19 ga watan Afrilu.

Mourinho, mai shekaru 51, ya taya murna ga alkalin wasa Mike Dean bayan an doke Chelsea da ci 2-1 a filin wasa na Stamford Bridge.

Wata sanarwar hukumar FA ta ce, kalamin Mourinho ya zubar da kimar wasan, don haka aka tuhumi kocin dan kasar Portugal da aikata ba daidai ba, a baya ma Mourinho ya gaza samun nasara a wata kara da ya daukaka game da wata tarar fam dubu takwas da aka ci shi kan wani laifin daban.

Sai dai Kocin ya musanta aikata ba daidai ba, a yayin karawar da Aston Villa ta cinye kungiyarsa 1-0 a ranar 15 ga watan maris, inda aka ganshi ya nufi alkalin wasa Chris Foy yana kokarin magana da shi kafin a kore shi waje, lamarin da ya saba wa dokokin FA.

Hukumar kula da wasanni ta ce Mourinho ya aikata laifi kuma hukuncin da aka yi masa na nan daram.

Karin bayani