Za a bayyana tawagar 'yan Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana cigaba da tafka mahawara a Ghana dangane da 'yan wasan da zasu je Brazil.

Mai horar da 'yan wasan Ghana Kwesi Appiah na shirin bayyana tawagar 'yan wasan da zasu gasar cin kofin duniya a Brazil bayan ya ce tuni yana da masaniyar 'yan wasan da yake da niyyar tafiya da su.

Sai dai hakan bai sa an daina tafka mahawara ba, game da 'yan wasan da zasu sami tafiya Brazil din da kuma dalilan da zasu yi tasiri kan zaben wanda zai tafi.

Appiah dai shike jagorantar 'yan wasan zuwa Brazil a matsayin mai horar da 'yan wasan kasar dan asalin Ghanan a karon farko da zai ja ragamar 'yan wasan Black Stars a gasar cin kofin duniyar.

Kwesi Appiah ya kai wannan matsayin ne bayan da ya taimakawa Milovan Rajevac na Serbia a shekarar 2010 a lokacin da Ghana ta kai zagaye na biyu, kuma ya ce ya koyi darasi sosai daga waccar gasar da zai taimaka masa wajen yin zabi gabanin gasar cin kofin duniya a Brazil.