Manchester City ta lashe gasar Premier

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Magoya bayan City na murnar lashe gasar

Manchester City ta lashe gasar Premier ta Ingila a bana, bayan ta doke West Ham da ci biyu da nema a wasan karshe na gasar da suka buga a ranar Lahadi.

City ta lashe kofin sau biyu kenan a cikin shekaru uku.

Samir Nasri ne ya ci wa Manchester City kwallon farko a yayinda Vincent Kompany ya ci wa kungiyar kwallo ta biyu.

Liverpool ta kasance ta biyu a gasar bayan ta doke Newcastle da ci biyu da daya.

Kungiyoyi uku sun nuste sun koma gasar Championship watau Cardiff da Fulham da kuma Norwich.

Sakamakon sauran wasannin gasar:

  • Cardiff 1 - 2 Chelsea
  • Fulham 2 - 2 Crystal Palace
  • Hull 0 - 2 Everton
  • Liverpool 2 - 1 Newcastle
  • Man City 2 - 0 West Ham
  • Norwich 0 - 2 Arsenal
  • Southampton 1 - 1 Man Utd
  • Sunderland 1 - 3 Swansea
  • Tottenham 3 - 0 Aston Villa
  • West Brom 1 - 2 Stoke

Karin bayani