Lescot na shirin barin Manchester City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lescott ya bar Everton zuwa ManCity a shekarar 2009

Dan wasan zakarun Premier Manchester City Joleon Lescott na shirin barin kulab din bayan ya shafe shekaru biyar a ciki.

Lescott mai shekaru 31 ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa wannan wani lokaci ne mara dadi sosai a gare shi.

Ya ce 'ina godiya ga duk wanda keda alaka da kulab din, kuma wani lokaci ne da nayi wasa mai armashi a rayuwata ta.

Tsohon Manajan City Mark Hughes ne ya kawo Lescott daga Everton a wata yarjejeniyar £22m a watan Agustar shekarar 2009.

Dan wasan na Ingila ya bayyana fiye da sau 100 a kulab din Manchester City.