Ferdinand zai bar Manchester Utd

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ya yi wasansa na karshe a Old Trafford, inda Man U ta tashi canjaras 1-1 da Southampton a wasan karshe a gasar premier ta bana

Rio Ferdinand zai bar Manchester United a lokacin bazara, bayan da aka ki bashi sabon kwanturagi.

Tafiyar dan wasan bayan mai shekaru 35, za ta kawo karshen zamansa a kulob din inda ya buga wasanni 454, kuma ya jefa kwallaye 8 a raga.

Ferdinand ya ce "Bayan shekaru 12 masu kayatarwa, na yanke shawarar yanzu lokaci ya yi na matsa gaba."

Sashen wasanni na BBC ya fahimci cewa dan wasan zai ci gaba da taka leda, amma a yanzu ba a san kulob din da zai koma ba.

An kuma yi imanin cewa Manchester ta fada masa cewa tana son ya dawo, domin zama daya daga cikin tsofaffin zaratan kungiyar, a matsayin karrama gudunmawar da ya bayar yayin zamansa kulob din.

Dan wasan ya taimaka wa Man U lashe gasar premier guda shida da gasar zakarun Turai biyu da kofin Champions daya da kuma kofin duniya na kungiyoyin wasanni guda daya.