Rodgers na Liverpool ya samu sabon mukami

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi shekaru 20 ana bada wannan kyautar

An bayyana Shugaban kulab din Liverpool Brendan Rodgers a matsayin shugaban kungiyar manajojin gasar Ingila.

Rodgers mai shekaru 41 ya jagoranci kulab din zuwa matsayi na biyu a gasar Premier League da kuma sake komawa gasar Champions League yayin da suka kammala da maki biyu a bayan Manchester City.

Rodgers, shine manajan kulab din Liverpool na farko da ya lashe wannan kyauta a shekaru 20 da aka yi ana bada kyautar.