Gwarzayen Premier:Suarez da Pulis

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Suarez ya ci kwallaye 31 a gasar premier

An bayyana dan wasan gaban kungiyar Liverpool Luis Suarez a matsayin gwarzon kakar wasanni ta bana yayin da Tony Pulis na Crystal Palace ya karbi kyautar manaja.

Suarez mai shekaru 27 ya kuma ci kwallaye 31 a gasar Premier wadda hakan ya taimakawa Liverpool kai wa mataki na biyu ya kuma ci kyautar Golden Boot saboda yawan kwallayensa a raga.

Pulis mai shekaru 56 ya karbi jagorancin Palace a watan Nuwamba inda ya taimakawa kulob din tashi daga matsayin na 19 zuwa na 11.