Terry zai zauna a Chelsea har 2015

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Terry ya buga wa Chelsea wasanni fiye da 600

John Terry ya sanya hannun sabon kwanturagin shekara guda da Chelsea.

Hakan na nufin Terry zai cigaba da taka kwallo a kulab din har zuwa shekarar 2015.

Dan wasan mai shekaru 33 ya taimaka wajen daga darajar kungiyar Chelsea a shekarar 1998, lokacin da ya shiga kungiyar yana matsayin karamin dan wasa daga West Ham.

Terry ya bugawa Chelsea wasanni sama da 600 da cin kofin Premier 3 da kofin FA 5 da kofuna 2 na league da kuma gasar kwararru a shekarar 2012.