Tottenham ta sallami kocin ta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana danganta Pochettino da kuma Shugaban Ajax Frank de Boer da sabon mukamin

Tottenham ta sallami mai horas da 'yan wasan ta Tim Sherwood bayan kulob din ya yi faduwar bakar tasa inda ya tsaya a matsayi na shida bayan kammala gasar Premier a kakar bana.

Shugaban kungiyar Daniel Levy ya ce da ma kwantaragin watanni 18 ne wanda zai kare a karshen wannan kakar, kuma wannan sakin layi muka yi amfani da shi don yanke wannan hukunci.

Ana danganta Manaja Southampton Mauricio Pochettino da kuma Shugaban Ajax Frank de Boer da mukamin mai horas da 'yan wasan.