Brazil 2014: Adidas ya kirkiri Brazuca

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Brazuca' za a buga a gasar cin kofin duniya

A shirye-shiryen da ake na fara gasar cin kofin duniya a Brazil, shahararren kamfanin nan na Adidas ya kirkiri wata tamaula mai suna Brazuca.

Za a yi amfani da kwallon a hukumance a gasar bana da za ayi a Brazil.

Kuma ita ce ta 12 da kamfanin Adidas ya kirkira a irin wannan gasa.

Kamfanin Adidas ya yi ikirarin cewa an inganta kwallon, sabanin wacce aka yi amfani da ita a gasar 2010 mai suna Jabulani wacce kuma ta fuskanci suka kwarai da gaske.