West Ham: Allardyce na shan suka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Allardyce na shan suka daga magoya baya

Kulab din West Ham United zai yanke shawara akan makomar Manaja Sam Allardyce nan da kwanaki 9 .

Shawarar zata biyo bayan ganawar karshen kakar wasanni da aka gudanar tsakanin Allardyce da kuma kwamitin gudanarwar kulab din.

A yanzu za su duba shirin manajan a kakar wasanni mai zuwa kafin su yanke hukuncin matakin da zasu dauka.

Allardyce dan shekaru 59 ya fuskanci suka daga magoya baya wadanda suke son a maye gurbinsa.