Park na Man U ya yi ritaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Park na fama da ciwo a gwiwar sa

Tsohon dan wasan tsakiyar Manchester United Park Ji-Sung ya yi murabus daga buga kwallon kafa yana da shekaru 33.

A shekarar 2005 ne Tsohon mai horas da 'yan wasan Manchester United Sir Alex Feguson ya dauki dan wasan haifaffen Koriya ta Kudu.

Sau hudu yana cin gasar Premier a Manchester United

Park, ya bayyana cewa ciwon da yake fama da shi a gwiwar sa na nufin cewa ba zai iya cigaba da wasa a matakin kololuwa ba.

Ya ce 'zan bar wasa ba tare da nadama ba'

Shine dan wasan nahiyar Asiya na farko da ya buga wasa a wasan karshe na gasar zakarun Turai.