Brazil:Scolari zai fuskanci tuhuma

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Luis FelipePortugal shine tsohon kocin Portugal

Kocin kasar Brazil Luis Felipe Scolari, zai fuskanci tuhuma kan aikata laifin kin biyan haraji, kamar yadda rahotanni ke bayyanawa daga kasar Purtugal.

Scolari mai shekaru 65 ya horas da kungiyar kwallon kafa ta Portugal daga shekarar 2003-2008.

A na kuma kallon zargin da ake masa na da alaka da zaman sa a can Portugal din.

A wata sanarwa da ya fitar, dan kasar Brazil din ya ce duk kasar da ya je aiki ya na bayyana kudaden da ya ke samu.

Zargin ya zo ne kasa da wata guda gabanin fara gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.