Man U zata tafka asarar £30m

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Manchester United ta sami sakamako mafi muni a bana

Babban mataimakin shugaban kungiyar Manchester United Ed Woodward ya bayyana cewa gazawar kulob din na zuwa gasar zakarun Turai zai janyo wa kulob din asarar tsabar kudi har sama da fam miliyan 30.

Manchester United ta kare wasan ta na bana inda ta tsaya a matsayi na 7, wanda shine sakamako mafi muni da kungiyar ta samu tun gasar shekarar 1989-90

Wood ya ce "mun kiyasta asarar da muka yi a gasar Premier ta kai £30. Ya kuma bayyana haka ne a taron masu zuba jari da suka kira.

BBC ta gano cewa, Louis Van Gaal dan kasar Netherland, ya amince da kwantaragin shekaru 3 inda zai maye gurbin David Moyes da kungiyar ta sallama cikin watan Afrilu.