Rwanda na bukatar Constantine

Image caption Constantine na da kwarewa a kwallon kafar Afirka.

Rwanda ta yiwa dan Burtaniya Stephen Constantine tayin zama sabon mai horar da 'yan wasan Kasar na shekaru biyu.

Hukumar kwallon kafar Rwanda na bukatar wanda zai gaji Eric Nshimiyimana wanda kwanturaginsa ke karewa a ranar 31 ga watan Yuli.

Constantine dan shekaru 51 yana da kwarewa a kwallon kafar Afirka.

Ya taba jagorantar Malawi daga watan Fabrairun 2007 zuwa watan Afrilun 2008.

Constantine zai tattauna da Kungiyar kwallon kafa ta Rwanda a ranar Alhamis.